{"title":"Sharhin Waƙar Garin Kwaki Ta Bage Ɗansala","authors":"Dano Balarabe Bunza","doi":"10.36348/sijll.2022.v05i12.007","DOIUrl":null,"url":null,"abstract":"An sanya wa takardar taken “Sharhin Waƙar Garin Kwaki Ta Bage Ɗansala” domin a yi sharhin turkenta da tubalanta da kuma salailan da aka samu a cikinta. An gudanar da hakan ta hanyar yin hira da makaɗin da wasu mutane da ke da masaniya kan waƙar ko abin da ke cikin waƙar, domin ganin an kammala takardar cikin nasara. An gano cewa babban saƙon da waƙar ke ɗauke da shi tarihi ne tare da ƙananan saƙonni daban-daban da ke cikinta ta fuskar bayani da kawo misalai gwargwadon hali. An kawo sakamakon binciken da aka gudanar wanda takardar ta hango da kuma kammalawa a ƙarshe.","PeriodicalId":122430,"journal":{"name":"Scholars International Journal of Linguistics and Literature","volume":"144 1","pages":"0"},"PeriodicalIF":0.0000,"publicationDate":"2022-12-22","publicationTypes":"Journal Article","fieldsOfStudy":null,"isOpenAccess":false,"openAccessPdf":"","citationCount":"0","resultStr":null,"platform":"Semanticscholar","paperid":null,"PeriodicalName":"Scholars International Journal of Linguistics and Literature","FirstCategoryId":"1085","ListUrlMain":"https://doi.org/10.36348/sijll.2022.v05i12.007","RegionNum":0,"RegionCategory":null,"ArticlePicture":[],"TitleCN":null,"AbstractTextCN":null,"PMCID":null,"EPubDate":"","PubModel":"","JCR":"","JCRName":"","Score":null,"Total":0}
An sanya wa takardar taken “Sharhin Waƙar Garin Kwaki Ta Bage Ɗansala” domin a yi sharhin turkenta da tubalanta da kuma salailan da aka samu a cikinta. An gudanar da hakan ta hanyar yin hira da makaɗin da wasu mutane da ke da masaniya kan waƙar ko abin da ke cikin waƙar, domin ganin an kammala takardar cikin nasara. An gano cewa babban saƙon da waƙar ke ɗauke da shi tarihi ne tare da ƙananan saƙonni daban-daban da ke cikinta ta fuskar bayani da kawo misalai gwargwadon hali. An kawo sakamakon binciken da aka gudanar wanda takardar ta hango da kuma kammalawa a ƙarshe.