{"title":"Matakan Ginin Karin Maganganu Na Mutane Masu Buƙata Ta Musamman","authors":"Mustapha Ahmad Shuni, Jamilu Ibrahim Mukoshy","doi":"10.36348/sijll.2023.v06i09.004","DOIUrl":null,"url":null,"abstract":"Wannan maƙalar ta yi nazarin karin maganganu na mutane masu buƙata ta musamman domin gano falsafar Bahaushe a kan wannan rukunin mutane da kuma tubalan da ake amfani da su wajen ginin karin maganganu masu alaƙa da su. Binciken ya yi amfani da manya da ƙananan hanyoyin tattara bayanai waɗanda suka haɗa da: Tattaunawa da lura ta kai-tsaye, da sauraren kafafen yaɗa labarai da ziyartar ɗakunan karatu na manyan makarantu don samun bayanai da karin maganganu masu alaƙa da mutane masu buƙata ta musamman. Sakamakon binciken ya yi nasarar fito da falsafar Bahaushe kan mutane masu buƙata ta musamman da kuma tubalai biyar da ake amfani da su wajen ginin karin maganganu na mutane masu buƙata ta musamman. A ƙarshe, maƙalar ta kammala da cewa, akwai jinsin mutane masu buƙata ta musamman a cikin Hausawa waɗanda ke da tunani da hikimomi da basira irin tasu. Sai dai, rashin kyakkyawar kulawa da kuma ƙyamar da wasu mutane ke nuna musu, ya sa suka zama tamkar saniyar ware a cikin al’umma. Saboda haka akwai buƙatar masana da manazarta su ƙara himma ga bincike a kan al’amurran da suka shafi waɗannan mutane domin inganta rayukansu da ciyar da al’umma gaba.","PeriodicalId":122430,"journal":{"name":"Scholars International Journal of Linguistics and Literature","volume":"356 1","pages":"0"},"PeriodicalIF":0.0000,"publicationDate":"2023-09-15","publicationTypes":"Journal Article","fieldsOfStudy":null,"isOpenAccess":false,"openAccessPdf":"","citationCount":"0","resultStr":null,"platform":"Semanticscholar","paperid":null,"PeriodicalName":"Scholars International Journal of Linguistics and Literature","FirstCategoryId":"1085","ListUrlMain":"https://doi.org/10.36348/sijll.2023.v06i09.004","RegionNum":0,"RegionCategory":null,"ArticlePicture":[],"TitleCN":null,"AbstractTextCN":null,"PMCID":null,"EPubDate":"","PubModel":"","JCR":"","JCRName":"","Score":null,"Total":0}
引用次数: 0
Abstract
Wannan maƙalar ta yi nazarin karin maganganu na mutane masu buƙata ta musamman domin gano falsafar Bahaushe a kan wannan rukunin mutane da kuma tubalan da ake amfani da su wajen ginin karin maganganu masu alaƙa da su. Binciken ya yi amfani da manya da ƙananan hanyoyin tattara bayanai waɗanda suka haɗa da: Tattaunawa da lura ta kai-tsaye, da sauraren kafafen yaɗa labarai da ziyartar ɗakunan karatu na manyan makarantu don samun bayanai da karin maganganu masu alaƙa da mutane masu buƙata ta musamman. Sakamakon binciken ya yi nasarar fito da falsafar Bahaushe kan mutane masu buƙata ta musamman da kuma tubalai biyar da ake amfani da su wajen ginin karin maganganu na mutane masu buƙata ta musamman. A ƙarshe, maƙalar ta kammala da cewa, akwai jinsin mutane masu buƙata ta musamman a cikin Hausawa waɗanda ke da tunani da hikimomi da basira irin tasu. Sai dai, rashin kyakkyawar kulawa da kuma ƙyamar da wasu mutane ke nuna musu, ya sa suka zama tamkar saniyar ware a cikin al’umma. Saboda haka akwai buƙatar masana da manazarta su ƙara himma ga bincike a kan al’amurran da suka shafi waɗannan mutane domin inganta rayukansu da ciyar da al’umma gaba.